Za mu tabbata mugayen yan Najeriya sun fuskanci hukunci

Nigeria News News

Za mu tabbata mugayen yan Najeriya sun fuskanci hukunci
Nigeria Latest News,Nigeria Headlines
  • 📰 DailyPostNGR
  • ⏱ Reading Time:
  • 23 sec. here
  • 2 min. at publisher
  • 📊 Quality Score:
  • News: 12%
  • Publisher: 59%

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da cewa “mugayen” ‘yan Najeriya za su fuskanci hukunci kamar doka ta tanada. Tinubu ya gargadi masu aikata mugayen laifuka, ko suna cikin Najeriya ko waje, cewa za a gurfanar da su gaban shari’a.

Shugaban kasar, wanda mai ba shi shawara kan tsaro na kasa, Nuhu Ribadu, ya wakilta, ya yi wannan bayani yayin bikin kammala karatun Kwasa-kwasan Executive Intelligence Management Course 17 a cibiyar nazarin tsaro da ke Abuja a ranar Asabar. Ya sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar. “Idan kai mutum ne mara gaskiya, ko kana Najeriya ko kana waje, kana cikin matsala. Za mu bi ka. Za mu gurfanar da kai a gaban shari’a,” in ji shi.

Shi ma da yake magana, darakta janar na hukumar DSS, Adeọla Ajayi, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta fuskanci matsalolin tsaro ba idan dukkan hukumomin tsaro suka yi aiki tare yadda ya kamata. Ajayi ya ce, “Tare za mu yi nasara. CDS da NSA sun kawo hadin kai ta wata hanya da ban taba gani ba a tsawon aikina. Dole mu yi aiki tare. “Darasinmu daga nan shi ne babu wata matsalar tsaro da za ta yi nasara a kanmu idan muka yi aiki tare.

We have summarized this news so that you can read it quickly. If you are interested in the news, you can read the full text here. Read more:

DailyPostNGR /  🏆 11. in NG

Nigeria Latest News, Nigeria Headlines

Similar News:You can also read news stories similar to this one that we have collected from other news sources.

Rahoton mutuwar mutum 10,000 a hannun sojoji: Najeriya ta gayyaci Amnesty Int’lShalkwatar tsaro ta kasa ta gayyaci kungiya kare hakkin dan Adam ta Amnesty International domin gabatar da hujjojin ta  kan zargin da ta yi na cewa mutane 10,000 sun mutu yayin da suke tsare a hannun sojoji tun bayan fara yakin Boko Haram a Arewa maso Gabas.
Read more »

Babu sansanin sojin wata kasa a Najeriya – Janar Christopher MusaShugaban hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, ya musanta rahotannin da ke cewa an baiwa Faransa izinin kafa sansanin soji a Najeriya.
Read more »

Gwamnati ta musanta bullar sabon nau’in cutar COVID-19 a NajeriyaMa'aikatar lafiya ta tarayya ta musanta bullar sabon nau'in cutar COVID-19 mai suna XEC a Najeriya.
Read more »

Jinkirin Jirage: Najeriya za ta hukunta kamfanonin jiragen sama masu laifiGwamnatin Tarayyar Najeriya ta hannun Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Sama, NCAA ta bayyana aniyarta na daukar matakin ladabtarwa kan kamfanonin jiragen sama da ke jinkirin tashi ba tare da gamsassun dalilai ba.
Read more »

Minista Idris: Tsarin haraji na Najeriya ya dade yana bukatar gyaraGwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tsarin haraji na Najeriya ya dade yana bukatar gyara. Ministan Harkokin Labarai da Wayar Da Kan Jama'a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a lokacin taron kasa da Hukumar Kwararru ta Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NIPR), reshen Jihar Kaduna, wanda aka gudanar a ranar Asabar a Jihar Kaduna.
Read more »

Shugaban NAHCON ya tabbatar da shirin kammala Hajj 2025 cikin lokaciShugaban NAHCON ya tabbatar da shirin kammala Hajj 2025 cikin lokaciShugaban Hukumar Hajj ta Kasa (NAHCON), Professor Abdullahi Saleh Usman, ya tabbatar da cewa Hukumar tana cikin shiri mai inganci domin kammala dukkan A karshe, ya tabbatar da cewa NAHCON na ɗaukar IHR a matsayin abokan hulɗa masu mahimmanci
Read more »



Render Time: 2025-03-13 15:32:13