Ma'aikatar lafiya ta tarayya ta musanta bullar sabon nau'in cutar COVID-19 mai suna XEC a Najeriya.
Ma'aikatar lafiya ta tarayya ta musanta bullar sabon nau'in cutar COVID-19 mai suna XEC a Najeriya. Ma'aikatar, a cikin wata sanarwa da mataimakin darekta na sashen labarai da juldar jama'a, Mista Alaba Balogun, ya sanyawa hannu, wanda aka rabawa manema labarai a Abuja ranar Asabar, ta yi kira ga 'yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu kuma su yi amfani da hanyoyin kare kai da aka saba dasu.
Wannan ya haifar da damuwa game da yiwuwar tasirinsa a kan tsarin kula da lafiya na duniya. Ma'aikatar ta jaddada cewa bincike ya nuna babu alamar wannan nau'in a cikin kasar nan. Duk da haka, gwamnatin tarayya ta inganta asibitoci da dakunan gwaji da kuma wuraren kebe masu cutar domin basu kulawa ta musamman, sai kuma naurorin taimakawa numfashi wato ventilators.
Nigeria Latest News, Nigeria Headlines
Similar News:You can also read news stories similar to this one that we have collected from other news sources.
Gwamnati ta gargadi asibitoci su kwana da shirin sabuwar cutar COVID-19Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi ga asibitocin kasar nan da sauran cibiyoyin lafiya su kasance cikin shiri kan sabon nau'in cutar COVID-19 na XEC, dake cigaba da bazuwa cikin sauri.
Read more »
Rahoton mutuwar mutum 10,000 a hannun sojoji: Najeriya ta gayyaci Amnesty Int’lShalkwatar tsaro ta kasa ta gayyaci kungiya kare hakkin dan Adam ta Amnesty International domin gabatar da hujjojin ta kan zargin da ta yi na cewa mutane 10,000 sun mutu yayin da suke tsare a hannun sojoji tun bayan fara yakin Boko Haram a Arewa maso Gabas.
Read more »
Babu sansanin sojin wata kasa a Najeriya – Janar Christopher MusaShugaban hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, ya musanta rahotannin da ke cewa an baiwa Faransa izinin kafa sansanin soji a Najeriya.
Read more »
IHRC ta zargi CBN da nuna wariya ga ma’aikatan masu alaka gwamnatin BuhariKungiyar kare hakkin Dan adam ta Duniya wato International Human Rights Commission (IHRC), zargi Babban Bankin Najeriya (CBN) da nuna bambanci tsakanin ma’aikata. Babban Daraktan Kungiyar na Najeriya, Ambasada Abdullahi Bakoji Adamu ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa ga manema labarai a Kano.
Read more »
Activate alert systems on COVID-like symptoms – FG advises tertiary hospitalsThe federal government has directed all the chief medical directors and medical directors of tertiary hospitals to immediately activate alert systems throughout the hospitals for a high index of suspicion in patients with COVID-like symptoms. This followed the circulation of the newly detected XEC COVID-19 variant in 29 countries globally.
Read more »
Ba za mu bar kudirin haraji ya zama doka ba – Hon. Ghali MustaphaDan majalisar wakilai, wanda ke wakiltar mazabar Albasu/Gaya/Ajingi karkashin NNPP Kano, Hon. Ghali Mustapha, ya ce kudirorin gyaran haraji za su cutar da al’umma. Da yake magana da manema labarai a Abuja a ranar Litinin, Hon. Mustapha, ya ce kudirorin, idan aka mayar da su doka, za su kara tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya.
Read more »