Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa akalla ‘yan Najeriya 10,000 ne aka tsare bisa laifukan karya dokokin shige da fice a kasashen Afirka da kasashen Turai a bana.
Sai dai ya yaba da irin gudunmawar da bakin haure ‘yan Najeriya ke bayarwa ga tattalin arzikin duniya, inda ya ce Najeriya ce ke kan gaba a yawan kudaden da ‘yan cirani ke samarwa a yammacin Afirka. Baya ga kudaden da ‘yan kasashen ketare ke fitarwa, ya ce ‘yan ci-ranin Najeriya sun zama jakadun na gari a fadin duniya wadanda suka yi fice a fannin fasaha, likitanci, wasanni, kere-kere da sauransu.
Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan jawabi a ranar Litinin yayin taron tattaunawa na shekara-shekara karo na 10 akan hijira zuwa wasu kasashen a fadar shugaban kasa dake Abuja. Ya ce, “Hijira tana da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa da ma duniya baki daya. A shekarar 2022 kadai, 'yan Najeriya dake ketare sun samar da kdalar Amurka biliyan 21.9.' Ya kara da cewa Najeriya kasa ce dake maraba da bakin haure inda sama da bakin haure miliyan 1.
Nigeria Latest News, Nigeria Headlines
Similar News:You can also read news stories similar to this one that we have collected from other news sources.
Vice President Kashim Shettima inaugurates Mamuda Group’s new factories: Advancing Nigerian industryThis landmark occasion represents another step forward in Mamuda Group’s journey of growth and innovation. With the inauguration of its new factories, Mamuda Group solidifies its role as a key contributor to Nigeria’s industrial and economic success
Read more »
Gwamnati ta musanta bullar sabon nau’in cutar COVID-19 a NajeriyaMa'aikatar lafiya ta tarayya ta musanta bullar sabon nau'in cutar COVID-19 mai suna XEC a Najeriya.
Read more »
Jinkirin Jirage: Najeriya za ta hukunta kamfanonin jiragen sama masu laifiGwamnatin Tarayyar Najeriya ta hannun Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Sama, NCAA ta bayyana aniyarta na daukar matakin ladabtarwa kan kamfanonin jiragen sama da ke jinkirin tashi ba tare da gamsassun dalilai ba.
Read more »
Minista Idris: Tsarin haraji na Najeriya ya dade yana bukatar gyaraGwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tsarin haraji na Najeriya ya dade yana bukatar gyara. Ministan Harkokin Labarai da Wayar Da Kan Jama'a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a lokacin taron kasa da Hukumar Kwararru ta Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NIPR), reshen Jihar Kaduna, wanda aka gudanar a ranar Asabar a Jihar Kaduna.
Read more »
Za mu tabbata mugayen yan Najeriya sun fuskanci hukunciShugaban kasa, Bola Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da cewa “mugayen” ‘yan Najeriya za su fuskanci hukunci kamar doka ta tanada. Tinubu ya gargadi masu aikata mugayen laifuka, ko suna cikin Najeriya ko waje, cewa za a gurfanar da su gaban shari’a.
Read more »
Tinubu ya jagoranci manyan ‘Yan Najeriya a Addu’o’in Fidau na Sheikh BelloShugaba Bola Tinubu, a ranar Lahadi, ya jagoranci manyan 'yan Najeriya wajen halartar addu'o'in Fidau na kwana uku domin sheikh, Muhydeen Bello, wanda ya Tinubu ya jagoranci manyan 'Yan Najeriya a Addu'o'in Fidau na Sheikh Bello
Read more »