Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya nada Kabiru Yakubu Jarimi a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin kananan hukumomi. Ibrahim Musa, babban sakataren yada labarai na gwamna Sani ne ya sanar da nadin a wata sanarwa a ranar Asabar. Jarimi shi ne tsohon shugaban karamar hukumar Kaduna ta Kudu.
Yana da digiri na biyu a fasahar bayanai, digirin difloma na biyu, da digiri na farko a kimiyyar kwamfuta. Musa ya ce nadin Jarimi ya yi daidai da shirin gwamnatin jihar na sauya fasalin karkara. “Kabiru Yakubu Jarimi gogaggen jami'in gwamnati ne kuma shugaba mai hangen nesa. Ya yi wa’adi biyu a matsayin zababben ahugaban karamar hukumar Kaduna ta Kudu,” in ji sanarwar.
“Sabon mai ba da shawarar yana da kwarewa a jagorancin dabarun tsarin mulki, manufofin gwamnati da warware rikice-rikice, karfafa matasa da bunkasar tattalin arziki, da kuma gudanar da harkokin kudi. “Jagorancinsa ya yi fice wajen samar da hadin guiwa tsakanin bangarori daban-daban don bunkasa tsaro, ilimi, kiwon lafiya, da ayyukan jin kai. “Yayin da gwamnatin Jihar ke kara hanzarta shirin sauya fasalin karkara tare da gina kananan hukumomi, gwamna Uba Sani na daukar kwararru don aiki da su.
Nigeria Latest News, Nigeria Headlines
Similar News:You can also read news stories similar to this one that we have collected from other news sources.
Gwamna Sani ya ba yan kwangila makonni 6 su kammala aikin titin KadunaGwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ba wa 'yan kwangilar da ke gudanar da aikin titin Ungwan Rimi-Kafanchan a cikin garin Ƙafanchan, karamar hukumar Jema’a ta jihar, wa’adin makonni shida su kammala aikin.
Read more »
Gov Uba Sani appoints Jarimi as Special Adviser on LG AffairsThe Kaduna State Governor, Senator Uba Sani, has appointed the immediate past Chairman of Kaduna South Local Government, Kabiru Yakubu Jarimi, as his Special Adviser on Local Government Affairs.
Read more »
Uba Sani appoints Kabiru Jarimi as SA on local government affairsUba Sani, governor of Kaduna state, has appointed Kabiru Yakubu Jarimi as his special adviser on local government affairs.
Read more »
Gwamna Sani: Gwamanoni ba zasuyi amfani da ’yan sandan Jiha don danne ’yan adawa baGwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya kwantar da hankula kan cewa idan aka kafa ’yan sandan jiha, gwamnonin jihohi ba zasuyi amfani da su wajen danne ’yan adawarsu ba.
Read more »
Governor Sani Sacks Kaduna’s Commissioner for Internal Security, Appoints New TeamGovernor Uba Sani of Kaduna State has dismissed Samuel Aruwan from his position as Commissioner for Internal Security in a major cabinet reshuffle. The decision comes after the Code of Conduct Tribunal asked for Aruwan's suspension over alleged false asset declarations. Aruwan’s replacement, James Atung Kanyip, and other new appointees were also announced.
Read more »
Gwamna Abdullahi Sule Announces 16 New Judges in Nasarawa StateGwamna Abdullahi Sule of Nasarawa State has appointed 16 new judges in a ceremony at the Supreme Court of Azara. The governor stated that the new judges will help improve judiciaries' efficiency and strengthen justice delivery in the state.
Read more »