Rundunar ‘yan tawaye karkashin jagorancin Hayat Tahrir al-Sham ta samu nasarar kawo karshen mulkin shugaba Bashar Al asad na shekaru 24. A safiyar yau Lahadi suka bayyana karbe iko da babban birnin kasar, Damascus, da kuma hambarar da Shugaba Bashar al-Assad.
Kawo yanzu ba a san inda Mr al-Assad yake ba, amma ‘yan tawaye sun ce ya tsere daga kasar. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wasu majiyoyin soji biyu da ke tabbatar da cewa jirgin shugaban ya fice daga Siriya zuwa wata kasa da ba a bayyana ba.
ta ruwaito cewa rundunar ‘yan tawaye karkashin jagorancin Hayat Tahrir al-Sham ta samu manyan nasarori a kwanakin baya, inda ta karbe manyan birane kamar Aleppo da Homs. A safiyar Lahadi, kwamandan HTS, Abu Mohammed al-Julani, ya ce za a ci gaba da kula da hukumomin gwamnati karkashin Firayim Ministan Mr al-Assad, Mohammad al-Jalali, har zuwa lokacin da za a mika ragamar mulki ga farar hula.
Nigeria Latest News, Nigeria Headlines
Similar News:You can also read news stories similar to this one that we have collected from other news sources.
Islamic rebels topple Syrian President, Bashar al-AssadThe regime of President Bashar al-Assad of Syria has been toppled by Islamic rebels in the country. The revels seized control of Damascus on Sunday, ending Assad's family's iron-fisted rule that has lasted for over 13 years of civil war in a seismic moment for the Middle East.
Read more »
BREAKING: Syrian opposition ‘overthrows’ President Bashar al-AssadThe armed opposition led by the HTS gained major victories in recent days taking over major cities like Aleppo and Homs.
Read more »
Bashar al-Assad 'flees' as Syrian rebels capture Damascus, topple governmentThe 24-year rule of Bashar al-Assad in Syria appears to have come to an end after rebel groups seized Damascus in the early hours of Sunday
Read more »
Yan majalisa zasu tattauna da babban lauyan kasa akan kudurin gyaran harajiMajalisar Dattawa ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro (Benue ta Kudu) da zai gana da Babban Lauyan Tarayya (AGF) a yau, domin shawo kan matsalolin da ke da nasaba da kudurin sake fasalin haraji. Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Barau I.
Read more »
LP za ta maka yan majalisarta da suka koma APC a gaban kotuJam’iyyar Labour Party ta sha alwashin daukar matakin shari’a kan mambobinta guda hudu na majalisar wakilai da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC. Mambobin da suka sauya shekar sun hada da Chinedu Okere, Mathew Donatus, Akiba Bassey, da Esosa Iyawe.
Read more »
Hukumar ‘yan sanda ta sallami manyan jami’ai 19 bisa laifuka daban-dabanHukumar 'Yan Sanda ta Kasa, PSC ta sallami manyan jami’ai 19 daga aiki, ciki har da mataimakan sufeto, sufeto na mataimaka, da sufeto mai daraja, bisa laifuka daban-daban da suka hada da sakaci da kin aiwatar da umarni.
Read more »