SABON JIDALIN RAƊAƊIN TSADAR RAYUWA: Darajar Naira ta zube, ta doshi N1,000 a Dala 1
Martaba da darajar Naira na ci gaba da zubewa a kasuwar ‘yan canji, ta yadda a ranar Laraba kaɗan ya rage a sayar da Dala 1 a Naira 1,000.A kasuwannin ‘yan canji dai sai da Naira ta faɗi ƙasa har ta kai an canji Dala 1 a Naira 910, su kuma ‘yan canji su na saye Naira 905.
Tun bayan da Gwamnatin Tinubu ta saki Naira a kasuwa domin ta yi kiwo ba tare da makiyayin da ke kula da ita ba, a kullum duk gonar da ta ratsa sai ta ci dukan tsiya. Sanadiyyar sakin Naira ba tare da linzami, tarnaƙi da dabaibayi a kasuwannin canjin kuɗi ba, tsadar rayuwa ta yi sama, malejin tsadar kayan masarufi ya cilla sama, haka duk wasu kayan da ake shigowa da su daga sai ƙara farashi su ke yi.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ake fama da raɗaɗin tsadar rayuwa, biyo bayan cire tallafin fetur da Gwamnatin Bola Tinubu ta yi. Tuni a kasuwannin yankunan karkara ake ci gaba da fuskantar tsadar kayan abinci, a gefe ɗaya kuma shiru ka ke ji, gwamnatin ta ƙi raba abincin tallafin da ta ce za ta raba.
Nigeria Latest News, Nigeria Headlines
Similar News:You can also read news stories similar to this one that we have collected from other news sources.
ABCON to FG: Stop Binance's operations in Nigeria to strengthen naira | TheCableThe Association of Bureaux De Change Operators of Nigeria (ABCON) says Binance, the cryptocurrency exchange company, must be stopped from operating in the country.
Read more »
Naira plunges at Forex marketsThe naira recorded a 3.3 per cent decline on Wednesday to close at N782.38 per dollar.
Read more »
Without working, I earned salaries after paying N1m for job slot at FCC, man tells probe panelRecall that on Monday, an ex-desk officer at the FCC, Haruna Kolo confessed to having received millions of naira from job seekers.
Read more »
UI gets N1bn for diaspora research centre“An allocation of 1 Billion Naira was provided in the Fund’s 2023 budgetary allocation under the Special Intervention Initiative of the Fund for the establishment of Diaspora Center for Research and Development'
Read more »
Dollar breaks N900/$ ceiling, heads to N950/$ at alternative markets | The Guardian Nigeria News - Nigeria and World NewsNaira crashed to as low as N910/$, yesterday, at the parallel market as the market switched to a panic mood. With the local currency breaking the N900/$ psychological ceilings, there are fresh concerns that the troubled currency is still far from bottoming out ...
Read more »
NIJAR TA TSOKANO TSULIYAR DODANNI: Ta hana UN, AU da ECOWAS shiga ƙasar, ta hana Amurka ganin Shugaban Mulkin Soja - Premium Times HausaKuma sun ƙara jaddada shirin su na tattaunawa da mahukuntan Nijar, wanda tawagar UN ɗin ta ce za ta ɗora kamar yadda jagoran ta ECOWAS
Read more »