Allah Yayi Alkawarin Bayar Da Nasara Ga Wanda Yayi Hakuri Da Kaddararsa, Mai Kyau Ko Marar Kyau, Daga Imam Murtadha Gusau

Nigeria News News

Allah Yayi Alkawarin Bayar Da Nasara Ga Wanda Yayi Hakuri Da Kaddararsa, Mai Kyau Ko Marar Kyau, Daga Imam Murtadha Gusau
Nigeria Latest News,Nigeria Headlines
  • 📰 PremiumTimesng
  • ⏱ Reading Time:
  • 100 sec. here
  • 3 min. at publisher
  • 📊 Quality Score:
  • News: 43%
  • Publisher: 78%

Allah Yayi Alkawarin Bayar Da Nasara Ga Wanda Yayi Hakuri Da Kaddararsa, Mai Kyau Ko Marar Kyau, Daga Imam Murtadha Gusau Manzon Allah (SAW) yana cewa: 'Ya kai dan Adam! Ka sani, da al’ummah baki daya za su taru, domin su cutar da kai da wani abu...,

Allah Yayi Alkawarin Bayar Da Nasara Ga Wanda Yayi Hakuri Da Kaddararsa, Mai Kyau Ko Marar Kyau, Daga Imam Murtadha GusauDukkanin kyakkyawan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah Madaukaki, taimakonsa da gafararsa muke nema; kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma ya batar to babu mai shiryar da shi.

“Shine wanda yayi halitta, kuma ya daidaita ta, kuma shine wanda ya kaddara abubuwa, kuma ya shiryar da su.”Ya ku bayin Allah masu daraja! A takaice dai ayoyin da suke tabbatar da wannan muhimmin rukuni na imani da kaddarar Allah da hukuncinsa, sun fi a kirga. Don haka, tilas ne ga duk wani Musulmi, wanda ya amsa sunansa na Musulunci, ya yarda cewa babu wani abu da zai faru cikin mulkin Allah, wanda sai daga baya Allah zai san shi. A’a, Allah ya rigaya, yasan komai tun fil-azal, kuma ya rubuta shi a allon kaddara, wanda yake wurinsa , kamar yadda yazo a cikin ingantaccen Hadisi, kuma kamar yadda Allah Madaukaki yake cewa:“Lallai hakan, yana cikin littafi, lallai hakan mai sauki ne a wurin Allah.

Ya ku ‘yan uwana! Ku sani, babu tilas ga dan Adam akan ayyukansa, a cikin akida ta Musulunci. Kuma mutum yana da dama da kuma zabi, ya aikata abin da ya ga dama, kamar yadda Allah Madaukaki yake cewa:“Kuma mun shiryar da shi hanyoyi biyu .” 4. Halittar Allah ga abubuwa, da samar da su da kudurarsa cikakkiya. Allah shine ya halicci kowane mai aiki da duk aikinsa, da duk wani mai motsi da motsinsa, da duk wani mai sukuni da sukuninsa.“Allah yana nan, lokacin da babu wani abu tare da shi. Kuma al’arshinsa ya kasance a kan ruwa. Kuma ya rubuta komai a cikn lauhul mahfuz. Kuma ya halicci sammai da kasa.”

“إن عِظَمَ الجزاءِ مع عِظَمِ البلاءِ، وإن الله تعالى إذا أحب قوما ابتلاهم، فمن رَضِيَ فله الرِضا، ومن سَخِطَ فله السُّخْطُ.” “Lallai gwaggwabar lada mai yawa mai tsoka tana tare da girman bala’i da jarabawa, kuma Allah Mai girma da daukaka idan yana son wasu mutane to sai ya jarrabesu; duk wanda ya yarda da jarrabawar Allah, to sai ya sami yardar Allah da nasararsa, kuma duk wanda yayi fushi da kaddarar Allah, to shi ma sai Allah yayi fushi da shi.

To idan duk muka san wannan, zamu samu natsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarmu baki daya. Sannan kuma babu wani abun da zai tayar muna da hankali, komai gurmansa, kuma ko mai hadarinsa.

We have summarized this news so that you can read it quickly. If you are interested in the news, you can read the full text here. Read more:

PremiumTimesng /  🏆 3. in NG

Nigeria Latest News, Nigeria Headlines

Similar News:You can also read news stories similar to this one that we have collected from other news sources.

Group adopts Yayi as 2027 Ogun guber candidateGroup adopts Yayi as 2027 Ogun guber candidateThe Nation Newspaper Group adopts Yayi as 2027 Ogun guber candidate
Read more »

Oyo Assembly summons Miyetti Allah leaders over attack, killings in IwajowaOyo Assembly summons Miyetti Allah leaders over attack, killings in IwajowaOyo State House of Assembly has summoned the leaders of Miyetti Allah Cattle Breeders Association in the State. The lawmakers asked the leaders of the association to appear before it and explain roles played during the recent attack that took place in Iwajowa Local Government Area.
Read more »

Insecurity: Miyetti Allah vows to fight scourge in NigeriaInsecurity: Miyetti Allah vows to fight scourge in NigeriaTHE National Association of Miyetti Allah Kautal Hore, a Fulani Socio Cultural Organisation, yesterday, vowed to remove bad eggs among them and others involved in criminal activities across the country.
Read more »

Miyetti Allah sets up security outfit to help Tinubu’s govt fight criminalityMiyetti Allah sets up security outfit to help Tinubu’s govt fight criminalityA Trusted Nigerian Newspaper
Read more »

Miyetti Allah launches security outfit to address insecurity in NigeriaMiyetti Allah launches security outfit to address insecurity in NigeriaThe Miyetti Allah Kautal Hore has announced its commitment to supporting the Federal Government in its efforts to combat the escalating security challenges across the nation.
Read more »

Miyetti Allah takes proactive measures against insecurity in South EastMiyetti Allah takes proactive measures against insecurity in South EastA Nigerian newspaper and Online version of the Vanguard, a daily publication in Nigeria covering Nigeria news, Niger delta, general national news, politics, business, energy, sports, entertainment, fashion,lifestyle human interest stories, etc
Read more »



Render Time: 2025-02-15 10:13:59